A wata hirar da ya yi da tashar talabijin ta CBS da ke Amurka, Sarkin ya ce ba yau mahukuntan Saudiyya suka fara wannan ba, domin ko a shekarar 1996 lokacin da mahaifinsa ya karbi ragamar tafiyar da kasar sun bukaci yin haka.
Rikici tsakanin Qatar da Saudiyya ya barke ne a ranar 5 ga watan Yuni, kuma har yanzu bangarorin biyu sun kasa zaunawa kan teburi guda domin tattauna matsalar domin shawo kanta.